<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Converse, Charles Crozat (1834-1918), Scriven, Joseph Medlicott (1819-1886)</author>
<title>Alhajai na Almasihu LW364</title>
<lyrics>[V1]
 1) Alhajai na Almasihu
 Hanyar ɗaya mu ke bi
 Kome wuya, kome ƙunci
 Za mu ƙasar alkawali.

[V2]
 2) Hasken Yesu Ubangiji
 Yesu walƙiya wajenmu
 Yana koran duhun hanya
 Yana cika zuciyarmu.

[V3]
 3) Ɗaya ne Ubangijinmu
 Ɗaya ce bangaskiyarmu
 Ɗaya ne kuwa begenmu duka
 Ɗaya kuma yancinmu.

[V4]
 4) Waƙar masu bi ce ɗaya
 Kome dubban bakinmu
 Ɗaya ce zumuntar hanya
 Ɗaya ce jawabinmu.

[V5]
 5) Ɗaya ce sujadar taron
 Cikin ƙasar sama can
 Inda Alahnmu Mai Ҡamna
 Yana mulki abadan.</lyrics>
<hymn_number>364</hymn_number>
</song>